Kamar yadda wani masanin al’amuran duniya dan kasar Kenya mai suna Adhere Cavince ya fada, “Manufar kasar Amurka ta zama shingen hana farfadowar tattalin arzikin duniya, da ci gaban kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka.
Hauwa Bala, matar marigayi Isah Bala, ɗaya daga cikin mafarautan da wasu gungun ’yan sa-kai suka kashe a yankin Uromi, da ke Jihar Edo, ta haihu bayan rasuwar mijinta. Ta haifi yarinya mace
Antony ɗan ƙasar Brazil ya zura ƙwallo huɗu, sannan ya taimaka an ci ƙwallo huɗu a wasa 12 da ya buga tun bayan zuwansa aro da zai zauna zuwa ƙarshen kakar bana. Wata majiya daga Manchester United ta ce Betis ce take biyan kusan kashi
Sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin na gwamnati kuma Reuters ta ruwaito, ta zo ne a lokacin da Nijar ke mai da hankali kan tsaron man fetur a cikin ƙasar, sakamakon tashin hankali na cikin gida.
Tawagar ta hada da masana girgizar kasa, da injiniyoyin gine-gine, da ma’aikatan bincike da ceto, da jami’an lafiya, da jami’ai masu aiki da karnuka domin gano mutane. Kuma sun tafi da kayayyakin aiki kamar naurorin gano mai rai, da na rusa gini, da kayayyakin lafiya.
Abin ya faru ne da karfe 10:45 na safe bayan an gama Sallar Eid da Limamin Gombe ya jagoranta, kuma gwamnan jihar Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar suka halarta.
Harin dai wanda aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike.