Gani Ya Kori Ji - Matar Mamaci Ta Haihu Bayan Rasuwar Mijinta, Ta Nemi Taimako.
Labaran Duniya

Matar Mamaci Ta Haihu Bayan Rasuwar Mijinta, Ta Nemi Taimako.

Matar Mamaci Ta Haihu Bayan Rasuwar Mijinta, Ta Nemi Taimako.


Hauwa Bala, matar marigayi Isah Bala, ɗaya daga cikin mafarautan da wasu gungun ’yan sa-kai suka kashe a yankin Uromi, da ke Jihar Edo, ta haihu bayan rasuwar mijinta.

Ta haifi yarinya mace ba da daɗewa ba, amma yanzu ta rage ita kaɗai ce wadda za ta ke jaririyar da sauran ‘ya’yanta guda shida, ba tare da wata hanyar samun kuɗin shiga ba.

A cikin yanayi na kuka, Hauwa ta bayyana damuwarta game da halin da ta samu kanta bayan rasuwar mijinta.

Ban san yadda zan kula da ‘ya’yana ba yanzu. Mijina ne yake ɗaukar nauyin komai,” in ji ta.

Marigayin Isah Bala ne ke ɗaukar nauyin duka buƙatun iyalinsa, har da kuɗin makarantar ‘ya’yansu.

Muhammad MI Sardauna

admin@ganiyakoriji.com

PUBLISHER/ PRESENTER www.ganiyakoriji.com (FILM&TV PRODUCER/DIRECTOR) Journalist/Writer.

Follow Me:

Comments