Labaran Duniya
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, Ya Kai Ziyara Ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, Domin Nuna Alhini Kan Kisan Gilla Da Aka Yi Wa Matafiya Dyan Arewa A Uromi

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi.
Harin dai wanda aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah.
Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike.
Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin.
Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun aiki a gaban doka a cewar Gwamnan.
Sanata Barau ya amsa da yabon matakan gwamnatin Edo, yana mai cewa.
Dole ne a ci gaba da yin Adalci domin hana irin wannan bala’i a nan gaba.
Yansandan sun kara da cewa za su ci gaba da yaki da duk wani yunkurin tayar da tarzoma a jihar.
Gwamnan Edo ya kuma yi kira ga al’umma da su yi haƙuri, yana mai jaddada cewa jihar ba ta yarda da ‘yan daba ko dakar doka a hannu ba.
Edo ta kasance gida ne na zaman lafiya ga dukkan al’ummar Nijeriya, kuma za mu kiyaye wannan tarihi a cewar Gwamnan
Comments