Gani Ya Kori Ji - MENENE CIWON SUGAR (DIABETES) DA KUMA HANYOYIN MAGANCE TA
Kiwon Lafiya

MENENE CIWON SUGAR (DIABETES) DA KUMA HANYOYIN MAGANCE TA

MENENE CIWON SUGAR (DIABETES) DA KUMA HANYOYIN MAGANCE TA

Likitoci sun bayyana wannan cuta a matsayin gazawar wani sinadari da ake kira insulin ko kuma rashin sinadarin ga bakidaya a jiki, wanda aikinsa shine tunkuda sugan dake cikin jinin mutum zuwa inda yakamata yaje a jiki.

Masana na cewa wannan ciwo ne da aka fi gado a mafi yawan lokuta, amma a wasu lokuta ko mutum beyi gado ba yana iya kamuwa dashi.

        Alamomin ciwon sugar

1)Yawan jin kishirwa
2)Yawan laulayi
3)Yawan jin gajiya
4)Yawan rama
5)Yawan jin yunwa
6)Yawan fita fitsari

         NAU’IKAN CIWON SUGAR
 
Akwae nau’in farko da ake kira da type 1 : wanda suke fama da irin wannan nau’in yawanci basu gada daga wajan zuri’arsu ba, masu wannan nau’in sune mafi karanci a duniya kuma anfi samunsa a jikin kananan yara ko kuma shekara 20 zuwa kasa.
Akwae nau’in type 2: Wannan nau’i yafi yawa tsakanin mutane kuma yafi addabar mutane dake tsakanin shekara 20 zuwa 79. Wannan nau’in yafi yawa a bangaren gado, yana yawan bin zuri’ar mutane daga uwa ko uba ko kawu da dai sauran dangi.

            ABUBUWAN DAKE KAWO CIWON SUGAR.

1)Gado
2)Kiba ko nauyi ya wuce misali
3)Rashin motsa jiki
4)Cin abinci mai yawan sugar

 Shin ana iya warkewa daga wannan cutar??

Masana a fannin lafiya sunce ba kasafai ake warkewa tas ba, sai dai akan iya samun saukin da akan manta ma wane yana da cutan idan aka bi matakin da ya dace.

Ana iya kiyaye wannan cuta ne ta hanyar kauracewa abubuwan da kan iya ta’azarata da kuma bin hanyoyin da ke samar da saukin ciwon.

                 SHAWARWARI

Kungiyar lafiya ta amurka ta bada shawarwari kan cewa dan shekara hudu zuwa shida ba’a son yasha sikari sama da biyar a rana.
Dan shekara bakwai zuwa goma kar ya wuce cokali shida na shayi kwantankwacin gram 24. Daga shekara shadaya zuwa manya wa’anda basu wuce kilo 30 ba, cokali bakwai yafi dacewa su sha a rana. Sai namiji babba lafiyayye cokali tara yakamata ya sha kwantankwacin gran 38 a rana yayin da babbar mace aka shawarce ta da kada tasha sama da cokali shida daidai da gram 25. Amma ba’a fadi adadin da masu cutar ya kamata su rika sha ba a rana saboda ko wanne da irin yadda matakin cutar yake a jikinsa.
Abincin da yake da fiber wato mai hade da dusa da wanda ba’a cashe ba shi ne abu na farko daya kamata ace mai cutan sugar ya mayar da hankali a kai.

Hakanan nau’ikan gayyayaki irinsu ugu, alayyaho, gurji, caras, lattas, da dai sauransu, sai ya’yan itace da suma suna matukar taimakawa wajan kwantar da wannan cuta a jikin dan adam. Yakamata mai cutan ya guji abinci mai dauke da sinadarin glucose a cikinsu kamarsu fura, tuwo, waina, shinkafa, rogo da dai sauransu.

Abunda yakamata mutane su sani shine ciwon sugar ba ciwo bane da ake iya yadawa cikin al’umma ta hanyar mu’amalar yau da kullum wato ba communicable disease bane.

Muhammad MI Sardauna

admin@ganiyakoriji.com

PUBLISHER/ PRESENTER www.ganiyakoriji.com (FILM&TV PRODUCER/DIRECTOR) Journalist/Writer.

Follow Me:

Comments