Labaran Duniya
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Ce Zai Sanar Da Karbar Harajin Kwastam Na Ramuwar Gayya Kan Kayayyakin Kasashe Daban Daban, A Jiya Laraba

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce zai sanar da karbar harajin kwastam na ramuwar gayya kan kayayyakin kasashe daban daban, a jiya Laraba, a matsayin wani sabon mataki karkashin yunkurinsa na ta da “yakin harajin kwastam” a duniya.
Matakin da shugaba Trump ke son dauka ya janyo damuwa a duniya.
Kamar yadda wani masanin al’amuran duniya dan kasar Kenya mai suna Adhere Cavince ya fada, “Manufar kasar Amurka ta zama shingen hana farfadowar tattalin arzikin duniya, da ci gaban kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka.
Za a maye gurbin kasuwannin kasar Amurka da na sauran kasashe da yankuna, lamarin da zai mai da Amurka saniyar ware. Cikin dogon wa’adi, jama’ar kasar Amurka za su tafka mafi yawan hasara, kana mutanen duniya za su fara ganin wani sabon yanayin da kasar Amurka da ba ta iya babakere a duniya.
Comments