Gani Ya Kori Ji - Kundin Bayanai

Latest News

Rundunar ƴan Sanda A Jihar Ribas Ta Ce Ta Kama Wani Mutum Mai Suna Michael Kan Zarginsa Da ɗaba Wa Abokinsa Uchenna Wuƙa Har Lahira, Bayan Da Ya Zarge Shi Da Sata Masa Waya.

An bayyana cewa lamarin ya faru ne a titin Egede da ke mile 2 a jihar ta Ribas a ranar Laraba. Uchenna dai ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ya kai wa abokina ziyara wanda aka ce sun daɗe suna abota. Bayan an garzaya da shi asibiti ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa - yayin da ƴan sanda suka cafke wanda ake zargi da aikata laifin.

Amurka Ta Saki Wani ɗan Rasha Da Aka Samu Da Laifin Zambar Kuɗaɗe, A Wani ɓangare Na Musayar Fursunoni Tsakanin ƙasashen Biyu.

Alexander Vinnik na gudanar da wani kamfanin musayar kuɗaɗen kirifto, wanda masu shigar da ƙara a Amurka suka ce na ɗaya daga cikin manyan masu taimaka wa masu laifi a faɗin duniya wajen turawa da kuma ajiye kuɗaɗe.

Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Rasu Bayan Wata Tirela Ta Murƙushe Su A Gadar Muhammadu Buhari Da Ke Yankin Hotoro A A Jihar Kano

Wani ganau ya bayyana cewa kimanin mutane 20 da kaya ne ke cikin motar a lokacin da ta kife, inda wasu daga cikinsu suka rasu suka jikkata. Shi ma wani ganau mai suna Shu’aibu Hamisu, ya ce tirelar ta fito ne daga hanyar Maiduguri tana kokarin sauya hanya zuwa titin Zariya Road, amma ta kwace wa direbanta.

Ranar 13 Gawatan February Na Ko Wacce Shekara Rana Ce Da Hukumar Raya Al'adu Ta Majalisar Dinkin Duniya Wato UNESCO Ta Ware Domin Duba Tasirin Da Radio Ta Ke A Rayiwar Al'uma Kai Tsaye.

Kamar yadda kowa yani radio da matukar muhimmanci ga ci gaba kakuma wayar da kan mutane irin cigaban da duniya ke samu. Gami da samar da shirye shirye masu iliman tarwa, nishadantarwa, da debe kowa baya ga nishadi da wasu ke samu sakamakon sauraran radio da suke.

A Rungumi Hakuri A Zaman Aure ‘Yan’uwa Mata.

HAKURI, Yana da matukar riba a rayuwa, ba ma a zamantakewar aure kadai ba, abin da yake damun wasu ma’auratan shi ne gaggawa da rashin hakuri, za ka ga mutum yana fadin cewa yana cikin matsala amma kuma abin mamaki shi ne ba zai iya hakuri akan matsalar ba.

Hamas Ta Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Isra'ila

Rahotanni sun ce Hamas ta amince da sharuddan tsagaita bude wuta da Isra’ila, wadda ke kai hare-hare ta kasa da ta sama a Gaza a matsayin ramuwar gayya kan harin ranar 7 ga Oktoba, 2023. A lokacin farmakin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra’ila, ta yi garkuwa da mutane da dama a Isra’ila inda ta kawo su Gaza, wanda hakan ya haifar da ramuwar gayyar da ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa kimanin 46,000.

Yadda Jami'an Tsaro Suka Shiga Gidan Shugaban ƙasar Koriya Ta Kudu Suka Kamo Shi

Yoon Suk Yeol ya zamo shugaban ƙasa na farko mai ci da aka taɓa tsarewa a Koriya ta Kudu bayan da jami'ai masu bincike suka kawar da shinge da karya wayar da ta kange gidan domin su kamo shi. Ana binciken Yoon mai shekaru 64 ne dai bisa tuhumar tayar da tarzoma a ƙasar bayan da ya gaza sauya dokokin ƙasar da na tsarin mulkin soja a watan Disambar 2024 wani abu da ya jefa ƙasar cikin ruɗani