Gani Ya Kori Ji - sin

Latest News

Yanzu Haka Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Dauki Wani Mataki Na Bazata Kan Harajin Da Ya Kakaba Kan Wasu Kayayyaki Sai Dai Ban Da Kayan Da Ke Shiga ƙasar Daga China.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai za a ƙara wanda aka lafta kan kayan China zuwa kashi 125%. Donald Trump ya kuma zargi China

Jimilar Mambobi 118 Na Tawagar Jami’an Bincike Da Ceto Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin Ta Isa Birnin Nay Pyi Taw Na Myanmar, A Ranar Lahadi.

Tawagar ta hada da masana girgizar kasa, da injiniyoyin gine-gine, da ma’aikatan bincike da ceto, da jami’an lafiya, da jami’ai masu aiki da karnuka domin gano mutane. Kuma sun tafi da kayayyakin aiki kamar naurorin gano mai rai, da na rusa gini, da kayayyakin lafiya.

Fitaccen ɗanbindigar Nan Da Ya Yi Fice Wajen Garkuwa Da Mutane Don Neman Kuɗin Fansa, Wanda Ya Addabi Yankunan Jihar Zamfara Da Wasu Yankunan Jihar Katsina, Wato Kachalla Isuhu Yellow, Wanda Aka Fi Sani Ya Cimma Sa'i

Lamarin ya auku ne da yammacin Alhamis, bayan daɗewa da ya yi yana wasan-ɓuya da jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ƴanbindiga a arewacin Najeriya da suke nemansa ruwa a jallo.

Tuni Aka Gudanar Da Jana'ida R Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina Haj. Safara'u Umar Bare-bari A Garin Radda Dake Jihar Katsina

A ranar Lahadi 23 ga watan Maris 2025 aka gudanar da jana'izar marigayi Haj. Safarau Umar Bare-bari, Mahaifiya ga Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda, inda aka binne ta a garin Radda da ke karamar hukumar Charanci, a jihar Katsina.

Rundunar ‘yan Sandan Nijeriya Ta Ce Ta Samu Nasarar Kama Wata Mata Da ‘mai Safarar Makamai Da Miyagun ƙwayoyi’ Ga ‘yan Ta’adda A ƙoƙarinta Na Kai Kayayyakin Jihar Katsina

sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Talata mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a Olumuyiwa Adejobi, ta ce an kama matar mai shekara 30 da kayayyakin da suka haɗa da jigidar harsasai 124 da aka ƙunshe a cikin wata jarkar man-ja mai cin lita biyar.

Tsohon Firaministan Lebanon__Rashin Fahimta Da Shakku Daga Waje Ba Za Su Iya Dakatar Da Ci Gaban Kasar Sin Ba

A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya.

Hukumar Kula Da Gandun Daji Da Filayen Ciyayi Ta Kasar Sin Ta Bayyana Cewa, A Cikin ‘yan Shekarun Da Suka Gabata, Namun Dajin Kasar Ta Sin Sun Karu Yadda Ya Kamata Ba Tare Da Cikas Ba.

Adadin manyan dabbobin Panda ya karu daga kimanin 1,100 a shekarun 1980 zuwa kusan 1,900 a yau. yayin da yawan damisar dusar kankara ya kai fiye da 1,200. Sai kuma adadin giwayen daji nau’in Asiya da ya karu daga fiye da 150 zuwa sama da 300.