Labaran Duniya
Gwamnan Rikonkwarya Na Jihar Ribas, Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, Ya Nada Shugabannin Kananan Hukumomi 23 Na Jihar, Duk Da Umarnin Da Wata Babbar Kotun Tarayya Ta Bayar Na Hana Shi Yin Hakan

Gwamnan rikonkwarya na jihar Ribas, Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya nada shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar, duk da umarnin da wata babbar kotun tarayya ta bayar na hana shi yin hakan.
Nadin wanda ya fara aiki daga ranar 7 ga watan Afrilu, 2025, wani bangare ne na gwagwarmayar neman mulki tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar dokoki masu biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike.
To sai dai al’ummar jihar na neman a bayyana musu yadda za a tafiyar da kasafin kudin jihar bisa la’akari da cewa babu ‘yan majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Wadannan nade-nade da kantoman ya yi sun janyo zarge-zargen cewa ya yi watsi da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.
Rahotanni sun ce al'ummar jihar na nan na nuna rashin jin dadinsu a game da abubuwan da ke faruwa a harkar tafiyar da gwamnatin jihar.
Gwamnatin nrikon kwaryar nan dai na nan na kakkabe dukkan wasu abubuwa da tsari na dimokradiyya a jihar.
A ranar 18 ga watan Maris din 2025, ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Comments