Gani Ya Kori Ji - Yanzu Haka Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Dauki Wani Mataki Na Bazata Kan Harajin Da Ya Kakaba Kan Wasu Kayayyaki Sai Dai Ban Da Kayan Da Ke Shiga ƙasar Daga China.
Labaran Duniya

Yanzu Haka Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Ya Dauki Wani Mataki Na Bazata Kan Harajin Da Ya Kakaba Kan Wasu Kayayyaki Sai Dai Ban Da Kayan Da Ke Shiga ƙasar Daga China.

Yanzu haka shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki wani mataki na bazata kan harajin da ya kakaba kan wasu kayayyaki sai dai ban da kayan da ke shiga ƙasar daga China.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai za a ƙara wanda aka lafta kan kayan China zuwa kashi 125%.

Donald Trump ya kuma zargi China da nuna rashin girmamawa da kuma zaluntar Amurka.

Kafin haka, China ta sanar da ƙara haraji kan kayan Amurka da ake shiga da su China zuwa kashi 84% - inda Chinar ta zargi Amurka da amfani da dabarar "zare idanu" kan ƙasashen duniya.

Muhammad MI Sardauna

admin@ganiyakoriji.com

PUBLISHER/ PRESENTER www.ganiyakoriji.com (FILM&TV PRODUCER/DIRECTOR) Journalist/Writer.

Follow Me:

Comments