Gani Ya Kori Ji - Hukumar Ƙungiyar Cigaban ƙasashen Yammacin Afirka, Ecowas Ta Nuna Damuwa Kan Rashin Jituwar Da Ta ɓalle Tsakanin ƙasar Mali Da Maƙwafciyarta Algeria.
Labaran Duniya

Hukumar Ƙungiyar Cigaban ƙasashen Yammacin Afirka, Ecowas Ta Nuna Damuwa Kan Rashin Jituwar Da Ta ɓalle Tsakanin ƙasar Mali Da Maƙwafciyarta Algeria.

Hukumar Ƙungiyar cigaban ƙasashen yammacin Afirka, Ecowas ta nuna damuwa kan rashin jituwar da ta ɓalle tsakanin ƙasar Mali da maƙwafciyarta Algeria.

lamarin da ya kai ga ƙasashen biyu janye jakadunsu daga junaa cikin wata sanarwa da ta fitar yau babban birnin tarayya Abuja.

Ecowas ta ce Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin ƙasar Mali da kuma Algeria, kamar yadda za a iya gani a jerin sanarwar da dukkanin ɓangarorin biyu suka fitar.

A madadin ƙasashen da ke da wakilci a cikinta, Ecowas na nuna matuƙar damuwarta kan lamarin.

 Yayin da take kira ga Mali da Algeria da su mai da wutar da suka fito da ita cikin kubenta wajen yayyafa wa wutar da ta kunno kai ruwa.

Tare da bukatar su buɗe hanyoyin tattaunawa sannan su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya na yanki da nahiya wajen warware saɓanin ra'ayin da ke tsakaninsu.

A makon da ya gabata ne dai Algeria ta harbo wani jirgi maras matuƙi mallakin sojojin ƙasar Mali, wanda ta ce ya karya dokokin kan iyakar ƙasarta.

Yayin da kasar Mali ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadanta da ke Algeria kiranye.

haka nan ma ƙasashen da suke ƙungiyar giyar yankin Sahel na AES, sun bi sahun Mali ta hanyar ɗaukar irin wannan mataki.

Lamarin da ya sanya ita ma Algeria ta yi wa jakadunta da ke Mali da Jamhuriyar Nijar kiranye, sannan ta ce za ta jinkirta tura jakadanta zuwa Burkina Faso, wadda ita ma mamba ce a ƙungiyar ta AES.

Muhammad MI Sardauna

admin@ganiyakoriji.com

PUBLISHER/ PRESENTER www.ganiyakoriji.com (FILM&TV PRODUCER/DIRECTOR) Journalist/Writer.

Follow Me:

Comments