Kundin Bayanai
Rundunar ƴan Sanda A Jihar Ribas Ta Ce Ta Kama Wani Mutum Mai Suna Michael Kan Zarginsa Da ɗaba Wa Abokinsa Uchenna Wuƙa Har Lahira, Bayan Da Ya Zarge Shi Da Sata Masa Waya.

Rundunar ƴan sanda a jihar Ribas ta ce ta kama wani mutum mai suna Michael kan zarginsa da ɗaba wa abokinsa Uchenna wuƙa har lahira, bayan da ya zarge shi da sata masa waya.
An bayyana cewa lamarin ya faru ne a titin Egede da ke mile 2 a jihar ta Ribas a ranar Laraba.
Uchenna dai ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ya kai wa abokina ziyara wanda aka ce sun daɗe suna abota.
Bayan an garzaya da shi asibiti ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa - yayin da ƴan sanda suka cafke wanda ake zargi da aikata laifin.
Rundunar ƴan sandan jihar ta Ribas ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin zuwa yanzu.
Comments